Mai girma tsohon gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa Dacta Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci mambobin jam’iyyarsu na jihar Kano da su mara baya ga gwamna Abba Kabir Yusuf domin ciyar da jihar Kano gaba.
Ganduje ya bayyana hakan ne yayin ziyarar taya murna da yan Majalisun jam’iyyar APC na jihar Kano suka Kai masa.
Yace duk da Abba ya fito daga jam’iyar adawa hakan baya nufin yan jam’iyar Baza tallafa masa wajen gudanar da ayyuka na ci gaban jihar.
Ya kara da cewa marawa gwamnatin baya ba yana nufin sun fita daga jam’iyar APC bane.