Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta ce ta kaɗu da jin yunƙurin sojoji masu juyin mulki a Nijar na tuhumar zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bazoum Mohamed da zargin babbar cin amanar ƙasa.
Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar sa’o’i bayan kalaman sojojin na yi wa Bazoum shari’a, Ecowas ta ce matakin wani takalar faɗa ne daga shugabannin sojin.
Ta kuma ce hakan ya ci karo da rahotannin da ake yaɗawa cewa sabbin masu mulkin Nijar ɗin sun nuna sha’awar bin hanyar masalaha don kawo ƙarshen dambarwar da ake ciki.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun ce sun tattara isasshiyar shaidar za a iya gurfanar da hamɓararren shugaban ƙasar Bazoum Mohamed a gaban kotu, bisa laifin cin amanar ƙasa.