Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihar Kano(NDLEA) tayi kira ga daliban ilmi dasu kaucewa shan magungunan dazasu hanasu bacci don suyi karatu.mataimakiyar shugaban a sashen wayar da Kai a jihar Kano
Hajiya Aisha Hameed ce ta bayyana hakan ga matan Aure wadanda suka samu nasarar sauke alqur’ani Mai tsarki a makarantar raudatut Ta’alimul islamiyya dake masallacin murtala inda ta bayyana cewa a matsayinsu na iyaye sai sun dage da sa idanu akan ya’yansu domin mafi yawan yara suna fara shaye shaye ne daga karatun don sunaso suyi karatun sai su gwada shan kwayoyi ko zasu hana su bacci wanda shine dalilin da kan zame musu jiki su rungumi shaye shayi har ta kaisu da zama yan’kwaya,
Ta kara da jan hankalin iyaye mata dasu yawaita bincika jakankunan ya’yansu domin anan suke boye kayan barna kuma wajibine susan yaran da suke mu’amala da ya’yansu domin hanasu tarayya da bata gari.
Anata bangaren shugabar makarantar malama Fatima Ahmad tsakuwa ta godewa mahalicci bisa nasarar data samu na gudanar da saukar alqur’ani da kaddamar da littafin da tayi Mai suna ADDU’A takobin mumini da kuma raba kyautuka ga Mashahuran mutane da suke hidimtawa maka rantar tare da yabawa da yadda jama’a suka amsa wannan gayyata.
Malama Fatima Ahmad tsakuwa ta bayyana cewa daliban mata hamsin da shida ne suka samu nasarar sauke alqur’ani Mai tsarki ta kuma ce littafin Dan karamin littafine amma ya kunshi mahimmam abubuwan da zasu amfani al’umma domin tayi duba na tsanaki akan yadda ake sakaci da ADDU’A a wannan lokacin da muke ciki.
Daga cikin wadanda suka karbi kyaututtukan sun hadar da maidakin Dan majalisar karamar hukumar kumbotso Hajiya Maryam inuwa dutse da uwar makarantar Hajiya mariya sunisi Mahdi dadai sauransu
sai kuma daliban da suke da shekaru kamar Hajiya Baba mai shekaru 67 da kuma malama Aisha muhd Mai shekaru 55 dukkaninsu sun godewa Allah daya nuna musu wannan rana kuma sun kira ga yan”uwansu mata dasu rungumi karatun Al-qur’ani don babu abin da ya Kaishi dadi.