Ku manta da wannan wahalar da kuke ciki ku kara zabar jam’iyar mu ta APC: Lafazin Tinubu ga yan Najeriya

Tsadar man fetur da yunkurin daina karban tsoffin kudade zagon kasa ake mini: Tinubu

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dogon layi a gidajen Mai da kara farashin man da kuma cukumurdar canza kudaden da mummunan yanayin da ake tsaka da shi na canza kudade a matsayin zagon kasa ga takarar sa.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yau Laraba lokacin da yake tsaka da gudanar da yakin neman zabe a jihar Osun.

Yace yan Najeriya na cikin halin ni’yasu a kan Man fetur sannan kuma an kara musu da wannan zulumi na canjin kudi.

Kana ya roki yan Najeriya da su daure wannan wahalar da suke ciki su manta da komai su zazzaga wa jam’iyar sa ta APC ruwan kuri’u donin yakai ga nasara.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments