Birtaniya da Faransa sun yi lale marhabin da matakin da Jamus ta dauka na bai wa Ukraine wasu shu’uman tankunan yaki samfurin “Leopard” domin ci gaba da fafatawa tsakaninta da Rasha.
Bayan tallafin tankar yaki da kasar Jamus ta baiwa Ukraine yau ake sa ran shi ma shugaban Amurka Joe Biden zai yi wa Amurkawa jawabi game da matsayar kasar kan aika wa Ukraine wadannan tankunan yakin.
An dauki tsawon makwanni ana yi wa Jamus matsin lamba kafin daga bisani ta amince da tura tankunan yakin kuma tuni shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya mika godiya ta musamman ga Berlin.
Kazalika Jamus ta amince wa sauran kasashen Turai kwastamominta da suka sayi ire-iren tankunan yakin daga gare ta, da su ma su tallafa wa Ukraine da tankunan kuma tuni Spain da Poland da Finland suka a fara amsa cewa, za su yi hakan.
Dama dai, dokokin cinikayyar sayen makaman Jamus sun kunshi cewa, dole kasar ta amince kafin kwastamominta da suka sayi makaman daga gare ta, su aika wa wata kasa ta daban.
Sai dai a yayin mayar da martaninta, Rasha ta yi tur da matakin na Jamus wanda ta bayyana a matsayin wani al’amari mai cike da hatsari, tana mai gargadin cewa, hakan ka iya sauya alkibilar yakin zuwa wani matakin gaba-da-gaba.
Ukraine ta dade tana fatan damkar wadannan shu’uman tankunan yakin da take kallo a matsayin wani abu mai matukar muhimmanci wajen tarwatsa sahun makiya.