Majalisar dattawan ta tafi hutu har zuwa wata guda domin bai wa ‘ya’yan damar yin yaƙin neman zaɓe a babban zaɓen da ke kararatowa.
Shugaban majalisar dattawan ƙasar Sanata Ahmad Lawan ne ya bayyana haka a zaman majalisar na ranar Laraba.
Sanata Ahmad Lawan ya ce majalisar ta ɗage zamanta daga ranar Laraba domin bai wa ‘yan majalisar damar yin yaƙin neman zaɓensu domin sake dawowa majalisar ko kuma taimaka wa jam’iyyunsu domin samun nasara.
A karshe yayi addu’ar Allah ya bai wa waɗanda ke son sake komawa majalisar dattawan nasara a zaɓen da ke tafe”.
Haka kuma ya yi kira ga hukumar zaɓen ƙasar da jami’an tsaro da su tabbatar da cewa an gudanar da sahihi kuma amintaccen zaɓe a ƙasa ba tare da samun tashin hankali ba.