Kotu ta yanke wa mutumin da ya kashe mahaifinsa saboda gida hukuncin kisa ta rataya a Akwa Ibom
Kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta rataya ko allurar gubaImage caption: Kotun ta yanke masa hukuncin kisa ta rataya ko allurar guba
Wata babbar kotun jihar Akwa Ibom ta yanke wa wani magidanci Moses Edo mai shekara 37 hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda ya kashe mahaifinsa.
Kotun wadda ta yi zaman shari’ar a jiya Talata, a yankin Æ™aramar hukumar Etinan ta jihar, da ke kudu maso kudancin Najeriya ta ce tun da har wanda ake tuhumar ya ambata da bakinsa cewa shi kansa ya hallaka mahaifin nsa ranar 29 ga watan Yuli a 2015 ba ta da wani dalili na Æ™in yanke masa hukuncin kisa.
Shi dai mutumin wanda É—an garin Ikot Ukobo ne a Æ™aramar hukumar Nsit Ubium ta jihar, yana sana’ar haya da babur ne wato achaÉ“a ko kabu-kabu.
Moses wanda shi ne babban ɗan mahaifin nasa mai suna Abdon Edo, ya sheda wa alƙalin kotun cewa ya bi marigayin da gudu ne har zuwa bayan tsohon gidan mahaifin, inda ya kama shi ya gwara kansa da bango, abin da ya yi sanadin mutuwarsa nan take kuma ya binne shi a kusa da kabarin ɗansa.
Ya sheda wa kotun, wadda ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kuma allurar guba, cewa suna rigima ne da mahaifin nasa a kan gida.