Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sanar da dage aikin kidaya wanda ta tsara za a gudanar dashi cikin wannan wata da muke ciki Zuwa watan mayu.
Ministan yada labarai da aladu Lai Muhammad shine ya bayyana dage war.
A gefe guda kuma gwamnatin ta amince da ware zunzurutun kudi Naira biliyan 2.8 domin siyan kayayyakin gudanar da aikin kidayar.