Kotu ta Aike da Shahararriyar ‘Yar TikTok Murja Kunya Zuwa Gidan Yari
Babbar kotun shari’ar musulunci dake filin hokey ta aike da murja Ibrahim kunya zuwa gidan gyaran Hali da tarbiya.
Wakilin aksata rawaito an gurfanar da ita a gaban kotun inda aka zargeta da laifukan bata suna, tayar da hankali da kalaman batsa da barazana.
Lauya mai gabatar da Kara lamido Abba soron dinki shi ne ya karanta mata kunshin tuhume-tuhumen da ake yi mata, Inda nan take ta musanta zargin.
Lauyan Murja Ibrahim Kunya Barr. Yasir Umar Musa ya nemi da a sanyata a hannun belli .
Alkalin babbar kotun shari’ar musuluncin dake zaman ta a filin hocky Mai Sharia Abdullahi halluru abubakar ya yi umarni da kai Murja zuwa gidan yari, sannan yace a mai da ita gaban kotu ranar 16 ga wata domin bayyana matsayar kotu Kan Neman bellin.
Lauyan Murja kunya ya nemi da’a kaita hisbah kafin waccan rana domin dai yimata wa’azi da nasiha kan zargin da akai mata.
A bakon da ya gabata ne Kadaura24 ta rawaito cewa rundunar yan sandan jihar kano ta kama Murja Ibrahim Kunya wacce ta shahara wajen yin kalaman batsa da zage-zage a dandalin sada zumunta na TikTok.