Jakadan kasar China dake kasar nan Cui Jianchun ya ziyarci jihar Kano, inda ya halarci bikin kaddamar da cibiyar tattara bayanai ta kasar tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
A yayin bikin, Cui ya bayyana cewa, a lokacin da ake murnar bikin Bazara na gargajiyar kasar Sin, an fara aiki da tashar jiragen ruwa mai zurfi ta Lekki, da sashe na farko na layin dogo mai aiki da lantarki a jihar ta Lagos, da cibiyar tattara bayanai ta kasa a Kano. Ko shakka babu Sin da Najeriya sun samu sakamako da yawa a fannin hadin gwiwarsu, wadanda suka faranta rayukan mutane sosai.
Cibiyar tattara bayanai ta Najeriya da ke Kano, wadda ke matsayin daya daga cikin ababen more rayuwa na zamani, tana aikin tattara bayanai, da rarraba ilmi da bayanai, da gabatar da goyon baya ta fuskar tsai da kuduri. Kamar yadda tashoshin jiragen ruwa, da layukan dogo suke yi, cibiyar za ta ba da muhimmiyar gudummowa wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Najeriya.
Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na Najeriya ya bayyana cewa, cibiyar tana matsayin irinta a matakin koli a duk fadin Najeriya, wadda mizanin ingancin bayanan da za ta tattara zai kai kaso 99.99 bisa dari. Kuma Najeriya tana alfahari da fara aiki da cibiyar.