Kamfanin mai na kasa NNPCL a yau alhamis ya ƙulla yarjejeniyar gyara da kamfanin Daewoo Engineering & Construction Nigeria Limited domin gyara matatar mai ta Kaduna cikin gaggawa.
Matatar man ta Kaduna wadda ke tace gangar mai aƙalla dubu 100 a rana na daga cikin matatun Mai ta huɗu da ba sa samar da mai tsawon shekaru inda ƙasar ta dogara da shigo da mai daga ƙasashen ƙetare.
Tuni ita ma matatar mai ta Fatakwal aka soma gyaranta inda wani kamfani na Italiya ke gyaran.
Najeriya tana da matatun mai huɗu inda take da biyu a Fatakwal, ɗaya a Warri sai kuma ɗaya a Kaduna.