Kotun da ke sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa ta tsayar da ranar Litinin a matsayin ranar da za a karbi karar da aka shigar a kan Bola Tinubu da jam’iyar sa ta APC.
Jaridar Punch , ta ruwaito cewa a ranar Litinin mai zuwa takwas ga watan Mayu, za a fara shari’a inda jam’iyyun adawa ke rokon a soke nasarar da Bola Tinubu ya samu.
Mai ba jam’iyyar APC shawara a kan harkar shari’a, Ahmad El-Marzuq ya sanar da manema labarai a mako mai zuwa za a fara sauraron kara zuwa karshen wata.
El-Marzuq ya ce jam’iyar APC ta shiryawa shari’ar, za ta kare nasarar da ta samu a gaban kotun zabe.
Lauyan Tinubu, Tayo Oyetibo SAN ya tabbatar da lamari nan.
Karbar korafi ya kare Bincike ya nuna daga ranar 23 ga watan Afrilu, kotun ta daina karbar martanin korafi a kan zaben.
Lauyoyi su na masu neman kotu ta hana a rantsar da zababben shugaban kasa bisa ikirarin ba shi ne ya lashe zabe ba.