Gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa mara kishin jihar ne kadai zai iya hawa gireda har ya rushe sabon ginin kasuwar zamani da akai a tsohuwar Daula Otel dake birnin kano.
“Sama da shekaru 20 aka bar ginin na Daula Otel ba abun da ake a cikin sa , sai yara da aka bari suke shaye-shaye da Kuma barayi da suka Mayar da wurin wajen kwanan su da boye makamai, to meye laifin don mun yi wannan tsari da zai habbaka kasuwanci da tattalin arzikin jihar kano “.inji Ganduje
Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da je niyar ganin yadda aikin ginin kasuwar zamani ta Daula Otel ke gudana..
Yace gwamnatin Kano ta shiga yarjejeniya da yankawasu ne akan wurin saboda inganta kasuwanci da kuma samar da kudaden shiga ga gwamnati, ” wannan tasa muka baiwa yan kasuwa su Gina da kudin su ita gwamnati dama filin ta ne sai aka samar da tsarin da kowa zai amfana.
Ganduje ya kara da cewa a yadda gwamnatin jihar kano take cibiyar kasuwancin Nigeria dole ne samar da tsari irin na zamani domin kanon ta cigaba da rike kambunta na cibiyar kasuwancin Nigeria.
Yadda Sabon ginin na Daula Otel yake kenan
” Mun yi yarjejeniya da kamfanin da yake aikin Kuma duk wasu al’amura na shari’a mun riga mun cika su, don haka maga wanda zai ce zai hau gireda yace zai rushe wannan gini” . A cewar Ganduje