Yar,takarar jamiyyar P D P a majalisar wakilan kasar nan mai wakiltar kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa Hajiya Amina Ibrahim B.B. faruk, ta jaddada kudirinta na ganin ta ceto yankunan daga matsalolin dake addabarsu da suka hadar da karancin ruwan sha da zaizayar Kasa da rashin ayyukan yi ga Matasa dazarar ta samu Nasara a zaben shekara ta 2023 mai zuwa.
Hajiya Amina Ibrahim faruk,ta bayyana haka ne ga manema labarai dangane da zagayen gani da ido da ta yi a yankunan, domin baiwa alummar kananan hukumomin tabbacin zata cika wadannan kudurorin nata.
Tace Daga cikin kudurce kudurcen da take son cimma akwai, taimakawa tsaffin ma,aikata wajen hakkokinsu na fansho da tallafawa Matasa maza da mata da inganta harkokin ilimi da lafiya da tsaro da musamman wajen Samar da ayyukan yi, Wanda suna daga cikin abubuwan da suke haifar da matsalolin rashin tsaro a fadin kasar nan.
Tace,a zagayen mazabun da take yi ta fahinci abubuwa da dama da suke bukatar kulawar gaggawa, kamar Gidan Ruwa na joda da aka yi shakulatin bangaro da shi,Wanda idon yana gudana zai taimakawa manoman yankunan wajen yin noman rani da kuma,samarwa matane dubbunnai sana,oin dogaro da kai, yadda za su tsaya da kafafuwansu har ma su taimakawa wasu da ma samarwa musu ruwan sha tsaftatcce.
Haka kuma,ta koka dangane da yadda Gwamnati mai ci ta Kasa aiwatar da ayyukan ci gaba kamar titina da Samar da magudanan Ruwa a yankunan kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa abin ya ta,azzara Wanda yakamata a kawowa alummar wannan yanki dauki domin jin dadin alamuransu.
Daga karshe ta karyata rade radin da wasu suke yadawa cewa ta janye takararta ta zama yar,majalisa wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Gabasawa da Gezawa, inda tace,wannan magana Bata da tushe balantana makama.
Hajiya Amina Ibrahim b b faruk,tace,irin wadannan rade radin wasu ne daga cikin abokanan hamayya ta siyasa suke yada irin wadannan jita jitar domin kashewa magoya bayanta zuciya kasancewar itace mace tilo data fito domin nemowa alummar ta hakkokinsu.
Ta shawarci magoya bayanta da su yi watsi da irin wadannan karairayi da wasu mutane ke yi a matsayin zagon Kasa.