Mahukuntan yankin Falasdinu sun bukaci kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta binciki kisan da aka yiwa ‘yar jaridar Al-Jazeera Shireeen Abu Akleh da ake zargin jami’an tsaron Isra’ila da aikatawa.
Ma’aikatar wajen yankin na Falasdinu ce ta mikawa ICC bukatar bincike kan kisan na ‘yar jaridar inda Reuters ta ruwaito minista Riyad Al-Maliki na neman kotun ta kara zargin kisan na Abu Akleh kan tuhume-tuhumen keta hakkin dan adama da ke Isra’ila.
Ministan wajen na Falasdinu Al-Maliki ya ce lokaci ya yi da ya kamata Isra’ila ta gurfana kan ta’addancin da ta ke yiwa yankin da al’ummarsa tsawon shekaru.
A ranar 11 ga watan Mayun da muke ne, lokacin da Abu Akleh mai shekaru 51 ke daukar rahoton kan wani sumamen sojin Isra’ila a gab da sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin aka harbe ta kuma ta mutu nan take, wanda shaidun gani da ido ciki har da abokin aikin Akleh suka ce tabbas Sojin na Isra’ila ne suka dirka mata alburushi.
Falasdinawa sun yi amannar kisan Abu Akleh na sahun laifukan yaki da Isra’ila ke aikata musu wanda ya sanya su mika batun ga kotun ICC don bincike tare da tabbatar da adalci.
Sai dai, dai dai lokacin da Falasdinun ke damka batun ga ICC, Mustapha Barghouti sakatare janar na hukumar raya yankin ya ce kotun na kwar da kai game da halin da yankin ke ciki ta yadda aka shafe shekaru 13 suna mika masa bayanin aikata musu laifukan yaki ba tare da ta gudanar da bincike ba, amma cikin watanni 2 har ta tura masu bincike 42 zuwa Ukraine don binciken laifukan yakin da Rasha ta aikata