Mutane miliyan 278 daga cikin miliyan 828 da ke fama da yunwa a duniya na zaune ne a Afirka.
Hukumar Abinci da Aikin Noma ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa wannan adadi, wanda Bankin Raya Afirka (AfDB) ya tantance zai iya haura miliyan 310 a shekarar 2030.
Afirka na da kashi 65 cikin 100 na filayen noma da ba a taba ba.
Duk da cewa nahiyar na da isassun filayen noma da za ta ciyar da mutane biliyan 9 nan da shekarar 2050, tana shigo da abinci sama da tan miliyan 100 daga kasashen waje.
Rahoton halin da noma yake ciki a Afirka na shekarar 2022 ya bayyana cewa fannin noma a Afirka na bukatar dala biliyan 257 a duk shekara domin illar sauyin yanayi da juriya ga rikice-rikicen duniya.
Kasancewar kasashen turawa masu mulkin mallaka sun dora wa manoman Afirka nau’in noma daidai da bukatunsu kafin samun ‘yancin kai, har yanzu wannan dabi’a ta ci gaba da hana ci gaban nahiyar a fannin noma.
Bugu da kari, karuwar yawan jama’a, kayayyakin more rayuwa da kuma rashin saka hannun jari a aikin noma na kara zurfafa matsalar abinci a Afirka.
Kasancewar kungiyoyin ‘yan ta’adda sama da 30 da ke dauke da makamai a nahiyar kuma yana yin illa ga noma da kiwo.
Musamman a yankin Sahel da tafkin Chadi, miliyoyin mutane na fama da yunwa da karancin abinci saboda ta’addanci da barazanar tsaro.
Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuna cewa mutane miliyan 5.6 a kasashen Kamaru, Chadi, Nijar da Najeriya, dake tafkin Chadi, daya daga cikin yankunan da ake fama da rikici mafi dadewa a duniya, na fuskantar matsalar karancin abinci.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutane miliyan 18 ne ke fuskantar barazanar yunwa a yankin Sahel idan ba a dauki matakin kawar da matsalar karancin abinci da ake fuskanta sakamakon kungiyoyin ‘yan ta’adda ba.