yau Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon jajantawa ga shugaban kasar Pakistan Arif Alvi, bisa mummunan harin ta’addanci da ya auku a kasar sa.
Shugaba Xi ya jaddada cewa, Sin na matukar adawa da dukkanin nau’o’in ayyukan ta’addanci, tana kuma matukar Allah wadai da harin da ya haifar da rasa rayukan mutane da dama