Yadda kasar China ta cikawa kasashen Duniya baki akan kimiyya

Kasar China tayi kalaman gugar zana ga kasashen yamma ciki harda America inda tace tayi nisa a fagen cigaban kimiyya da fasaha.

Kalaman na zuwa ne a dai dai lokacin da Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar,  Mao Ning, take amsa tambayar Wani dan jarida da ya gabatar na cewa, “sau da dama wasu kasashen yammacin duniya ciki har da Amurka, sun yi ikirari tare da neman hana ruwa guda, kana wasu kasashen ketare sun nuna damuwa cewa, za a dakile ci gaban kimiyya da fasaha na kasar Sin

Hakan ce tasa kakakin ma’aikatar harkokin wajen Kasar China  Mao Ning ta yi karin haske kan wannan batun inda tace “babu wani takunkumi da zai iya toshe ci gaban kimiyya da fasaha na kasar Sin.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments