Kakakin Fadar Shugaban Kasar Russia Dmitriy Peskov ya bayyana kalaman Shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy na cewa “ya kamata NATO ta kaddamar da harin riga-kafi kan Rasha” a matsayin “kira ta fara yakin duniya”.
Peskov ya kimanta kalaman Zelenskyy ga kamfanin dillancin labarai na Russia RIA Novosti.
Peskov ya ce, bai kamata kasashen duniya su yi watsi da wadannan kalaman da aka ambata ba.
Ya ce, “Irin wadannan maganganu ba komai ba ne illa kira don fara sabon yakin duniya tare da mummunan sakamako da ba a tsammani.”
Peskov ya jaddada cewa Amurka, Birtaniya da Tarayyar Turai su mai da hankali kan wadannan kalaman.
Ya kuma ce, “Wadannan kasashen suna jagorantar Yukren kuma sun ce za su kare ta har zuwa karshe. Don haka dole ne su kasance masu alhakin aiyuka da maganganun wannan mutumin (Zelenskyy) da gwamnatinsa.”
Volodymyr Zelenskyy ya ce ne, “ya kamata NATO ta kaddamar da wani hari na riga-kafi kan Rasha domin kawar da yiwuwar amfani da makaman nukiliya”.