Daga Walid Hari.
Galatasaray na son dauko É—an wasan Portugal mai buga gaba Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, daga Manchester United a watan Janairu. (Fotomac – in Turkish)
Babban jami’i a Bayern Munich Oliver Kahn ya ce kungiyar Bundesliga na duba yiwuwar sayo Ronaldo a sabuwar kaka.(Bild, via Mail)
Wolves na sa ran tattaunawa da Julen Lopetegui a wannan makon, bayan da Sevilla ta kore shi a matsayin koci. (Sky Sports)
ÆŠan wasan tsakiya a Faransa N’Golo Kante, mai shekara 31, na ganin Chelsea ba ta son tsawaita zamansa a kungiyar, a daidai lokacin da kwantiraginsa ke shirin karewa a sabuwar kaka. (Footmercato – in French)
Inter Milan na fatan cimma yarjejeniyar tsawo kan Calhanoglu bayan kungiyoyi ciki har da Everton sun gagara sayen É—an wasan da ke buga tsakiya. (TEAMtalk)
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya musanta rade-radin cewa zai bar Haaland ya tafi Real Madrid. (Mirror)
Tsohon É—an wasa Ferdinand ya bukaci Man Utd ta saye É—an wasan Dortmund Bellingham