Gwamnatin kasar Mali tayi kudirin mayar da yan sanda da sauran jami’ai aikin Soja

Gwamnatin kasar Mali ta amince da wani sabon kudirin doka da ya tanadi shigar da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro cikin aikin Soja.

Da wannan siga, gwamnati za ta samu damar jibge ‘yan sandan a yankunan da sojoji suka kwato daga hannun ‘yan ta’adda domin tabbatar da tsaron al’umma da dukiyoyinsu da kuma hana dawowar kungiyoyi masu dauke da makamai.

Haka kuma tanadin dokar zai tilastawa jami’an kwana-kwana marawa sojojin da ke yaki da kungiyoyin masu ikirarin jihadi a bakin daga baya.

Ko da ya ke har yanzu wannan kudiri na bukatar amincewar majalisar rikon kwarya ta kasar, wacce ta kasance majalisar dokoki tun bayan da sojoji suka karbe mulki da karfin tuwo a shekarar 2020 kafin ya zama doka.

Matakin na daga cikin shawarwarin da aka amince da su yayin babban taron kasar da majalisar mulkin soji ta shirya a watan Disamban bara, a matsayin mafita daga rikicin kasar da yaki ci yaki cinyewa.

Da wannan mataki ‘yan sanda da sauran jami’an tsaron farin kaya za su ci moriyar albashi da sauran alawus dai-dai da sojoji.

Sai dai wannan sabon matsayi zai kuma hana su ‘yancin shiga yajin aiki ko shiga wata kungiyar kwadago ko kuma gudanar da zanga-zanga

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments