Gabatar da kasafin kudi yasa an tsananta tsaro a zauren Majalisa

Tsaro ya tsananta a ginin majalisar tarayyar Najeriya yayin da ake Sa ran Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudi na 2023 a yau Juma’a.

Ana ran cewa wannan shine karo na karshe da shugaban zai gabatar da kasafin inda zai mika na N19.76

Rahotanni sun bayyana cewa za a kayyade masu shiga zauren majalisar tun daga kan manema labarai, jami’an tsaro da ma’aikata don gujewa cunkoson.

Za a gabata da kasafin kudin a zauren  majalisar wakilai.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, majalisar dattawa da ta wakilai ana gyaran su hakan zai sa Buhari ya gabatar da kasafin a zauren majalisar wakilai na wucin gadi.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, yace an kammala duk shirin da za a yi domin bai wa ‘yan majalisar wurin zama tare da shugaban kasa da tawagarsa.

Za a kayyade yawan masu shiga majalisar saboda za a yi tantancewa ta musamman ga manema labarai, jami’an tsaro da ma’aikatan majalisar da zasu yi aiki yayin gabatar da kasafin.

An bukaci ma’aikatan da basu da hannu cikin tsarin su huta a gida yayin da bankuna da sauran kasuwancin dake gudana a wurin aka bukaci su rufe shagunansu.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments