Daga Walid Hari.
Darajar ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe za ta kai tsakanin euro milliyan 300 zuwa 350 idan wata ƙungiya tana sha’awar sayensa sai dai PSG ba ta da niyyar sayar da matashin mai shekara 23 bayan a rahotanni sun ɓulla cewa matashin yana son barinsu a watan Janairu. (Telegraph – subscription required).
Chelsea ta soma tattaunawa da ɗan wasan tsakiya na Ingila Mason Mount mai shekara 23 kan ƙulla sabon kwantiragi. (Standard)
Juventus na son sayen ɗan wasan Man U Diago Dalot inda matashin mai shekara 23 dan Portugal ke shirin barin ƙungiyar. (Calciomercato – in Italian).
Tottenham tana bibiyar dan wasan Brentford dan Ingila Ivan Toney da ƙungiyar Spurs ke ta zuba ido kan dan wasan mai shekara 26. (Football Insider)
Sir Jim Ratcliffe ya ce da ya shirya siye Man U a bazara amma iyalin Glazer ba za su sayar ba. (Financial Times, via Goal)
Kocin Wigan Leam Richardson na cikin shirin zama sabon kocin West Brom bayan da aka kori Steve Bruce. (Football Insider)