A wata kididdiga da gwamnatin tarayya ta fitar, ya nuna cewa ambaliyar ruwa ta yi sanadin mutuwar sama da mutane 500, inda kuma iftila’in ya shafi mutanen kusan miliyan daya da rabi a sassan kasar.
Babban sakataren ma’aikatar kula da ayyukan jin kai ta Najeriya Dakta Nasir Sani-Gwarzo ne ya bayyana haka a birnin Abuja, a yayin da yake karin bayani kan halin da ake ciki a Najeriya, dangane da ambaliyar da ta auku a sassan kasar.
Daktan ya ya ce jihohi 31 da kuma Abuja babban birnin kasar ambaliyar ruwan ta shafa, lamarin da ya kai ga lalata gonakin da fadinsu ya kai kadada 146,734, sai kuma gidaje 89,348 da suka lalace.
Kididdigar ta nuna cewar, daga cikin mutane miliyan 1,411,051 da ambaliyar ruwan bana ta shafa a Najeriya, mutane dubu 790,254 sun kauracewa gidajensu bisa tilas. Yayin da wasu kusan 1,546 suka samu raunuka.