Daga Walid Hari.
Liverpool na sa ido kan manyan ‘yan wasan Galatasaray ciki har da ɗan Faransa Sacha Boey mai shekara 22, da ɗan wasan Denmark mai buga tsakiya, Victor Nelson mai shekara 23, da ɗan Turkiyyar nan Kerem Akturkoglu mai shekara 23, sai kuma Yunus Akgun mai shekara 22.(Sun)
Paris St-Germain na zawarcin ɗan wasan Chelsea dan asalin kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, mai shekara 33, a sabuwar kaka. (Foot Mercato – in French)
Manchester United na da kwarin gwiwar cewa Cristiano Ronaldo mai shekara 37 zai ci gaba da zama a kungiyar a watan Janairu saboda alamomin da ɗan wasan ke nunawa.(ESPN)
Kocin Leicester City Brendan Rodgers ya ce yana Nazari kan ɗan wasan tsakiya na Ingila James Maddison mai shekara 25 a watan Janairu.(Mail)
Tottenham za ta biya Juventus £30.7m domin saye ɗan wasanta na gefe Dejan Kulusevski, mai shekara 22, a yarjejeniyar dindindin.( Italian)
Atletico Madrid ta sanya hannu kan yarjejeniyar £17.5m domin mallakar Grizman daga Barca.