Wata kotu ta aike da wasu matasa uku gidan ajiya da gyaran hali bisa zargin cin Zarafi

Daga Umar Ibrahim Sani Mainagge

mutanen uku da suka hada da : Nasiru ibrahim Isma’ila jibrin da Abbas uzairu da sauran mutum shida da suka gujewa kamun yansanda an gurfanad dasu ne a gaban Kotun shariar musulunci dake zamanta a Brigaid PRP wacce mai sharia mlm Nura Yusif Ahmad yake jagoranta bisa zargin hadin kai, tsoratarwa, cin zarafi wadannan laifuffuka sunyi hannun riga da sashi na 120,,227, da kuma sashi na 103 na kundin SPCL.

Directive Aliyu zainul abidina shine me gabatar da Kara na Kotun ya karanta musu kunshin tuhumar da ake musu na tare wani bawan Allah tareda cin zarafinsa harma suka tsoratar dashi cewar da bindiga da sun harbe shi har lahira kajifa mai sauraro ko meye yayi zafi idan ba abinda aka dora a wuta ba to saidai kammala karanta musu jerin gwanon tuhumen- tuhumen da ake musu ne take Nasir ya amsa laifinsa yayinda Isma’ila Jibrin da Abbas uzairu suka musanta.

Daga nan kuma me gabatar da kara ya roki Kotun tabasu wata ranar domin gabatar da shedu akan wadanda suka musa tareda yin rokon kafawa wanda ya shedun ikirari a karkashin sashi na 276 (A) na Acjl.

Bayan dogon nazari alkalin Kotun ya amince da rokon me gabatar da kara inda ya dage sauraron karar zuwa ranar 2/11/2022 domin fara sauraron shedu daga bangaren masu gabatar da kara

Munyi kokarin jin ta bakin wadanda ake zargin sai dai hakan ya gaza samuwa

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments