Falalar bikin Maulidin manzon Allah.
Daga Walid Y Hari.
Hakika haihuwar Manzan tsira Annabi S A W itace mafificiyar haihuwa a dukkanin wata hakittar ubangiji, haihuwarsa da Mahaifiyarsa mai suna Aminatu bint Wahabin tayi a ranar shabiyu ga watan Rabi’ul auwal a shekarar giwa, ta kawo sauyi matabbaci a fadin duniya, ya zamo fitila mai haska ko ina, ya zamo haske mai kore duhu, ya zamo jagoran da babu kamarsa, yazo da sauryin da duniya ke tafiya akai, ya zauna da Sahabbansa zama na jin dadi, kyautatawa, hakuri, da kyawawan halaye. Hakika manzan Allah yafi kowace halittar Allah daukaka, matsayi, da baiwa dama fifiko, shine mai babbar mu’ujiza ta Alqur’qni, mai khalifofin da suka bada rayuwarsu dan daukaka Addinin Allah.
Allah ka karawa Annabi wasila da fadila, sahabbansa Allah ka saka musu da alkairi, manyan malaman addini da shehunai Allah ka kara musu karama, iyaye da suke dora yaya kan tarbiya da kaunar Annabi Allah jaddada rahama a garesu.
Daga Hukumar Aksam munaiwa kowa murnar Maulidin Annabi S A W.