Hukumar dake sa Ido kan kadarorin gwamnati ta tabbatar da kama wasu da ake zargi yan bangar siyasa ne su 55 a yankin karamar hukumar kumbotso dake jihar Kano
Hukumar ta tabbatar da hakan ne ta bakin jami’in hulda da jama’a na Hukumar Ibrahim Abdullah
Abdullahi yace jamian su sun kai samame ne a dai-dai lokacin da suka sami labarin yan Daba su farmaki al’ummar yankin Na’ibawa tare da kone motocin mutane
Kazalika yace sun kwace muggan makami a hannun yan Dabar da suka kama