Uwargidan Shugaban kasar Türkiye, Emine Erdogan ta tattauna da Olena Zelenska, matar Shugaban kasar Yukren kan halin da mata da kananan yara da yaki ya shafa ke ciki, yayinda ta karbi bakuncinta a babban dakin taro na Vahdettin da ke Istanbul a ranar 2 ga watan Oktoba.
Emine Erdogan ta bayyana cewa, “Türkiye za ta ci gaba da gwagwarmayar diflomasiyya a dukkan fannoni domin samar da zaman lafiya.”
Ita kuwa Zelenska ta bayyana gamsuwarta da yadda Türkiye ta karbi bakuncin yara ‘yan kasar Yukren dubu 1 da 300 ba tare da iyali ba, ta kuma bukaci taimakon Emine Erdogan don kwashe kimanin yara 200 masu bukata ta musamman da kuma kawo su Türkiye.
An dauki tabbataccen mataki na farko kan bukatar neman taimako ta Zelenska kimanin watanni 2 bayan taron.
An kwashe marayu 34 daga gidan yara na Sonecko da ke birnin Odesa na Yukren zuwa Ankara, babban birnin kasar Türkiye.
Bayan duba lafiyarsu, an fara gudanar da aiyukan kula da yaran, wanda mafi kankanta a cikinsu yana da watanni 10 da haihuwa.
Olena Zelenska ta yada a shafinta na Twitter cewa, “Tsaron yara shine babban fifikonmu.” Ta kuma bayyana cewa kwashe yaran wani muhimmin misali ne na hadin gwiwa tsakanin matan shugabanni.