Xi Jinping ya gana da takwaran sa na kasar Cuba.

Da safiyar yau Jumma’a 25 ga wata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Cuba Miguel Diaz-Canel, wanda shi ne sakatare na farko na kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Cuba, wanda kuma a yanzu haka yake ziyarar aiki a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin.

A yayin shawarwarin, Xi ya ce, kasar Cuba, ita ce kasa ta farko da ta kulla huldar diplomasiyya  tsakaninta da kasar China daga yammacin duniya.

Xi yace huldar da ke tsakanin Sin da Cuba, ta zama abin buga misali a fannin hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen gurguzu, da kuma taimakawa juna a tsakanin kasashe masu tasowa cikin ingancii.

Ya ce kasar Sin na son kara zurfafa amincewar juna ta fuskar siyasa a tsakaninta da Cuba, da habaka hadin gwiwar a-zo-a-gani a tsakanin kasashen 2, da mara wa juna baya kan batutuwan da suke shafar babbar moriyar juna, da taimakawa juna a al’amuran kasa da kasa da na shiyya-shiyya, da raya kasa ta gurguzu mai halin musamman kafada da kafada, da kuma zurfafa huldar da ke yi tsakanin Sin da Cuba a sabon zamani.

A nasa bangaren, Miguel Diaz-Canel ya ce, ziyararsa ta nuna yadda Cuba ke bada muhimmanci kan raya huldar hadin gwiwa a tsakaninta da Sin.

Kazalika ya ce Cuba ta amince da yadda kwamitin tsakiyar jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karkashin shugabancin Xi Jinping, babban sakataren jam’iyyar, ya ba da gudummawa ta bunkasa tunani da aiki, a fannin raya kasar gurguzu musamman na kasar Sin a wannan  zamani, lamarin da a ganin Cuba, ya karfafa gwiwar dukkan sassan duniya masu kokarin samun ci gaba sosai

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments