Da yammacin jiya Jumma’a ne, kungiyar sada zumunta tsakanin Sin da kasashen ketare ta al’ummar kasar Sin, ta shirya taron tattaunawa tsakanin shugabannin matasan Sin da Afirka mai taken “Amfani da kuzarin matasa domin samar da kyakkyawar makomar bil Adama” karo na biyu ta kafar bidiyo, inda wakilan kungiyar sada zumunta tsakanin Sin da Afirka da wakilan matasan da suka zo daga kasar Sin da kasashen Afirka 35 suka halarci taron.
Yayin taron na jiya, matasan Sin da Afirka sun yi musanyar ra’ayoyi mai zurfi kan batutuwan da suka hada da “Hangen matasa: Muhimman al’adun da ake bukata yayin gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya”, da “Burin matasa: Ma’anar zamanintarwa irin na kasar Sin ga duniya”, “Aikin matasa: Managartan matakan da za a dauka domin tabbatar da muradun raya duniya” da sauransu.
Jakadan kasar Senegal dake kasar Sin brahima Sory Sylla ya yaba da sakamakon da kasar Sin ta samu wajen kawar da talauci, ya bayyana cewa, makomar duniya tana hannun matasa ne, don haka ya dace a samar da damammaki ga matasa domin su gina makomar duniya mai haske