Shugaban kasar Tunusia Kais Saied, ya bayyana matukar jin dadin sa da hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Tunisiya da China , inda ya nuna jin dadinsa, kan taimakon da kasar Sin ta dade tana baiwa kasarsa.
Shugaba Saied ya bayyana hakan ne, yayin ganawarsa da jakadan kasar Sin dake Tunisiya mai barin gado Zhang Jianguo.
Shugaban ya kara da cewa, sabbin damammaki na raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, za su gabatar da kansu ga taron koli na farko na Sin da kasashen Larabawa.
Saied ya jaddada cewa, kasar Tunisiya tana son yin hadin gwiwa tare da kasar Sin, wajen inganta alakar abokantakar dake tsakanin kasashen biyu, da sa kaimi ga inganta huldar dake tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangaren, Jakada Zhang ya ce, a ko da yaushe kasashen Sin da Tunisiya sun fahimci juna da kuma goyon bayan juna kan batutuwan da suka shafi moriyarsu da ma damuwarsu. Ya kara da cewa, kasar Sin na son hada kai da kasar Tunisiya, domin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi.