Yan fashin daji sun yi garkuwa da wata mata mai juna biyu tare da ɗiyarta matashiya a ƙauyen Akilibu da ke kan babban Titin Kaduna zuwa Abuja.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Asabar da ta gabata. Maharan sun nufi gidan mutanen kai tsaye domin sace su.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun kutsa cikin gidan ne da nufin sace Mijin matar amma sai suka taras baya gidan a lokacin.
Mazauna ƙauyen sun shaida wa jaridar cewa yan bindigan sun buɗe wuta da zuwansu domin tsorata mutane.
Maƙocin gidan da lamarin ya faru wanda ya nemi a ɓoye sunansa, yace maharan sun yi awon gaba da matar gidan, Adama, tare da ‘yayanta huɗu amma daga baya suka sako uku.
Ya ce: “Bamu iya bacci ba saboda harbin bindiga, sun shigo kauyen da ƙarfe 8:30 na dare lokacin mutane basu kwanta ba, kai tsaye suka tafi gidan mutumin, babban manomi amma akai sa’a ba ya gida.
” Wani mazaunin ƙauyen na daban, Ashir Akibu, yace yan fashin dajinn sun ɗauki mutanen da mamaki saboda sun zo ne tamkar jami’an tsaro.
Yan bindigan sun buɗe wa matafiya wuta An tattaro cewa bayan sace matar da ɗiyarta,
‘yan bindigan sun buɗe wa wata motar matafiya wuta lokacin da zasu keta ta kan babban Titin Kaduna-Abuja.