Mun shafe shekaru 29 babu likita a asibitin garin mu: Alummar garin Zakirai

Yadda al’ummar garin Zakirai a Kano su ka shafe shekaru 29 babu likita a asibitin garin

Daga Sadik Lamin Hassan

Al’ummar garin Zakirai da ke jihar Kano a arewacin Najeriya sun bayyana takaicinsu kan yadda su ka shafe shekaru 29 ba tare da gwamnati ta samar musu da babban likita a asibitin da aka gina tun lokacin mulkin gwamna Abdullahi Wase.

A shekarar 1994 ne gwamnatin jihar Kano ta gina asabitin na garin Zakirai kuma yana karkashin hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar sai dai har wannan lokaci babu babban likita a asibitin.

Garin Zakirai wanda shi ne hedikwatar ƙaramar hukumar Gabasawa na da nisan kilomita 42 daga birnin Kano kuma garin yana da yawan mutane fiye da dubu dari ɗaya, sai dai al’ummar wannan gari na fuskantar kalubale daban-daban musamman a ɓangaren kiwon lafiya.

Wakilin Aksam Media ya tattauna da wasu daga cikin mutanen wannan gari na Zakirai inda su ka bayyana irin kalubalen da su ke fuskanta musamman a lokacin da mata su ka zo haihuwa ko kuma wata larura da ta ke bukatar babban likita.

Muhammadu Auwal daya ne daga cikin shugabannin matasa a yankin ya bayyana cewa baya ga rashin babban likita a asibitin kuma suna fama da rashin ma’aikata da za iya bayar da tallafi ga kananan cututtuka.

Haka kuma Muhammad Auwal ya ce asibitin na Zakirai ya zama wata matattara ta ma’aikatan wucin gadi da su ke cin karen su babu – babbaka ta hanyar sayar da magani ga marasa lafiya akan farashin da su ka ga dama.

“Tun da aka gina wannan asibitin a zamanin mulkin gwamna Abdullahi Wase ba a taba samun babban likita ba. A shekarun baya ana tura dan bautar ƙasa a matsayin likita, amma a halin yanzu sai ma’aikata wucin gadi da su ma su ke bukatar horo da karin ilimi akan abin da su ka karanta”

“Idan marar lafiya ya je domin a duba lafiyarsa tare da rubuta masa magani, a nan sai abin da ya gani domin ma’aikatan wucin gadi ne za su rubuta maganin kuma su sayar maka akan yadda su ka ga dama”

Hakazalika Muhammad Auwal ya kara da cewa duk da irin rashin likita da kwararrun ma’aikata da kuma kayan aiki amma hakan bai hana gwamnati yiwa asibitin rijista da inshorar lafiya ba duk da cewa babu magani a asibitin.

“Asibitin yana cikin asibitocin da gwamnatin jihar Kano ta yiwa rijista a matsayin wanda ma’aikata za su da iyalansu domin a duba lafiyarsu, anna abin takaicin shi ne babu magani a duk lokacin da larura ta kai mutum ko iyalansa”

A lokacin haɗa wannan rahoton Aksam Media ta yi kokarin tuntubar babban sakataren hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano, Dr. Tijjani Hussaini sai dai bamu same shi. Sai dai wata majiya daga hukumar ta bayyana mana cewa gwamnatin jihar Kano ta dauki manyan likitoci guda 25 da za ta tura su asibitocin da su ke ƙarƙashin ta.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments