Kungiyar yan jaridu masu gabatar da shirye-shiryen masanaantar Kanywood sun koka da yadda masanaantar take asarar zunzurutun kudi har kimanin Dalar Amurka miliyan 600 a kowacce shekara.
Jawabin Hakan na kunshe ne ta cikin wani takaitaccen bayani da shugaban kungiyar Musa Sale Amin ya gabatar ta fefen bidiyo bayan kammala taron tattaunawa da suka gudanar a gidan Radio Najeriya Pyramid.
Amin yace lokaci yayi da zasu bayar da gudunmawar basirar da Allah ya hore musu wajan ganin an daina barin masanaantar ta Kanywood a baya.
A NASA bangaren Sakataran kungiyar Abdurashid Bello Imam bayan addu’a da fatan samun ci gaba da yayi yace zasu yi du mai yuwuwa wajan ganin sun kawo karshen wannan asara da ake tafkawa.