Chelsea na takaicin Tchouameni, Yaya Toure na horar da tawagar Ingila.
Daga Walid Hari
Mai kungiyar Chelsea kuma daraktan wasanni na kungiyar na wucin-gadi Todd Boehly na jin haushi da bacin rai da kuma mamakin yadda tsohuwar hukumar kungiyar da ta gabata ba ta nemi Aurelien Tchouameni ba kafin dan wasan na tsakiya ya tafi Real Madrid. (Sport – in Spanish).
Dan wasan tsakiya na Belgium Youri Tielemans, ya ce bai yi nadamar zama a Leicester City ba a bazaran nan duk da yadda ake danganta shi da tafiya Arsenal. (Sky Sports)
Sakamakon matsalar biza an bar dan bayan Manchester United Lisandro Martinez, da na Tottenham Cristian Romero, ba su samu damar shiga tawagar Argentina da za ta yi wasan sada zumunta biyu ba. (Mirror)
Tsohon dan wasan tsakiya na Manchester City da Ivory Coast Yaya Toure na taimaka wa tawagar Ingila ta ‘yan kasa da shekara 21, a shirin da take na karawa da Italiya da Jamus, a karatun da yake na kammala kwarewa a aikin kociya. (Mail)
Chelsea na zawarcin shugaban RB Leipzig Oliver Mintzla