Buhari ya ayyana Salihu Dembos a matsayin shugaban hukumar yada labarai ta NTA

Buhari ya ayyana Salihu Dembos a matsayin shugaban kafar yada labarai ta NTA

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mista Salihu Dembos a matsayin Babban Daraktan  talabijin ta kasa wato NTA.

Sanarwar nadin na kunshe ne cikin jawabin da Ministan yada labarai da aladu Lai Muhammad yayi a Abuja.

Ministan yace an nada Dembos ne bisa chanchantar sa duba da ya kwashe kimanin shekaru 20 yana aiki a gidan talabijin na NTA din.

A tsawon wannan lokaci ya rike Shugabancin tashar ta Lokoja da kuma ta Kano, kafin nadin kuma shine shugaban sashin cinikayya na hukumar

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments