Abin da ya sa ‘yan Zamfara ke fargabar sake rikicewar lamuran tsaro a yankunansu.
Daga Walid Hari
Al’ummar wasu yankunan na jihar Zamfara na cikin fargaba dangane da yiwuwar sake tabarbarewar matsalolin tsaro, tun bayan hare-haren da sojoji suka kai wa dabar kasurgumin ɗan fashin dajin nan Bello Turji.
Da dama mazauna jihar musamman yankin arewaci na cewa tun bayan hare-haren sojoji lamuran tsaro sun sake rincaɓe musu, musamman a kan titin Shinkafi, bayan hare-haren ramuwa da yaran Bello Turji suka kai.
An ce dan fashin ya sha da kyar, kuma tun bayan wannan harin ake zargin yaransa da kai harin huce takaici kan matafiya a masarautar Moriki da kuma wadanda ake tarewa a titin Kauran Namoda zuwa Shinkafi.
Sama da shekara 10 jihar Zamfara na fama da hare-haren ‘yan fashin daji da ya haddasa asarar rayuka da dimbin dukiya.
Kuma tun daga wannan lokaci ana samun gwamnatoci daban-daban da ke yakar matsalar da har yanzu aka gagara kawo karshenta.