Tun bayan ficewar tsahon gwamnan jihar Plateau Jonah Jang daga kwamatin yakin neman zaben Dantakarar Shugaban kasa na jam’iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar jam’iyar ta people democratic party take samun tasgaro a jihar.
Rahoton da Jaridar Premium times ta fitar tace Mista Jang dai ya janye Kiki ne daga kwamatin yakin neman zaben Atiku Abubakar a kokarin sa na marwa gwamna Wike baya a gefe guda kuma da adawa da kin saukar da shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu, yayi.
Sai dai kwamatin yakin neman zaben Atiku na jihar Plateau yace Mista Jang abin da yake fada raayin kashin kansa ne ba wait na jam’iyar PDP jihar Plateau ba