Daga Walid Hari
Fadar gwamnatin Najeriya ta warware zare da abawa game da dambarwar da ta taso kan bai wa gwamnatocin jihohi damar saye da kuma mika wa jami’an tsaro manyan bindigogi.
Damabarwar ta taso ne bayan da gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya yi ikirarin cewar gwamnati na nuna banbanci wajen aiwatar da wannan doka.
Sai dai fadar na cewa babu wata jihar kasar da aka ba izinin sayo makaman yaki masu sarrafa kansu domin raba wa kungiyoyinsu na samar da tsaro.
Fadar ta kuma ce an ba jami’an tsaro umarni su hukunta wadanda suka ki bin wannan umarnin.
Akarshe Malam Garba shehu Kakakin shugaba Buharin, ya yi kira ga jama’ar kasar da su guji mayar da batun tsaro ya koma tamkar na siyasa.