Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaɓa hannu kan dokar bayar da bashi ga ɗalibai a cikin satinsa na farko akan mulki, hakan ya sanya aka ƙara kuɗin makaranta a ƙasar nan.
Wahalar da iyaye da ɗalibai ke ɗaukar nauyin karatunsu su ke sha ta ninka sosai bayan an tsige tallafin man fetur da dakatar da mabambantan farashin canjin dala.
Ga jerin jami’o’in da kuɗin makarantarsu ya yi tashin gwauron zaɓe tun bayan sanya hannu kan dokar bayar da bashi ga ɗalibai wanda Legit.ng ta tattaro:
Jami’ar Ambrose Alli, Ekpoma, jihar Edo
Jami’ar wacce mallakin jihar Edo ce, ta sanar da ƙarin kuɗin makaranta da kaso 300% biyo bayan rattaɓa hannu kan dokar bayar da bashi ga ɗalibai.
Hakan ya sanya aka fara gudanar da zanga-zanga a makarantar, inda ɗalibai suka riƙa kiran da a kori shugaban jami’ar.
Yanzu a jami’ar ɗaliban fannin shari’a za su riƙa biyan N741,500 a maimakon N185, 000 da su ke biya a baya, yayin da ɗaliban fannin lafiya za su riƙa biyan N638,000 a maimakon N216,000 saboda ƙarin da aka yi.
Jami’ar Bayero, Kano (BUK) Jami’ar BUK na daga cikin jami’o’in gwamnatin tarayya da suka fara sanar da ƙarin kaso 100% na kuɗin makaranta.
Daliban da suka fito daga tsangayoyin Arts, Islamic Studies, Law, Social Sciences and Management Sciences za su biyan N95,000, sannan sabbin ɗalibai za su biya N105,000 a maimakon N39, 000 da aka biya a shekarar da ta gabata.
Jami’ar Benin (UNIBEN) UNIBEN na daga cikin jami’o’in tarayyar da suka sanar da ƙarin kaso 100% suma na kuɗin makaranta biyo bayan rattaɓa hannu kan dokar ba ɗalibai bashi da Shugaba Tinubu ya yi.
Ɗaliban kimiyya a jami’ar za su riƙa biyan N190,000 a maimakon N73,000 da ake biya a baya, yayin da ɗaliban da ba na fannin kimiyya ba za su riƙa biyan N170,000 a maimakon N69,000 da ake biya a shekarun baya.
Kudin Digiri Ya Yi Tashin Gwauron Zabi A wani labarin kuma, kuɗin karatun digiri da digirin digirgir ya tashin gwauron zabi a jami’ar Bayero da ke Kano, ana tsaka da kuka da tsadar rayuwa.
Jami’ar ta BUK ta yi ƙarin kuɗi masu yawa a fannin rajista da sayen ɗakin kwanan ɗalibai a makarantar.