Gwamnatin jihar Kano ta saka sabbin ma,aikatan da aka diba a gwamnatin da ta gabata ta Dacta Abdullahi Umar Ganduje sama da dubu goma halin tsaka Mai wuya.
Gwamna Abba ya bayar da sanarwa to bakin banban akanta na jihar Kano cewa an zara wadannan sababbin ma,aikatan daga tsarin karbar albashi a gwannatance har sai an tantancesu .
Yayin da wasu ma’aikatan suka kwashe watannin shida suna karbar albashi wasu kuma sun karbi na watanni biyu da masu wata daya dama wadanda basu taba karbar albashin ba.
A zantawar su da Wakili yar aksammedia sunce suna cikin tashin hankali da sanarwar kuma a don haka suke mika koken su.
A cewar su yanzu haka sun shiga sauke al’qur’ani da kuma azumtar wasu ranaku don neman kubuta daga furucin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Kazalika sun ce suna neman Karin addu’oi daga dai dai kun Al,umma domin Allah yasa gwamnatin tayi musu adalci a lokacin tantancewar
Sai dai a iya cewa wannan abu da gwamna Abba yayi ba wai sabon abu ne ba kasancewar duk gwamnan da zai mika mulki yakan yi wasu abubuwa da zasu bayar da cikas ga sabuwar gwamnati
Ko a baya Kwankwaso ya taba kirkirar kananan hukumomi a dai dai lokacin da zai mika mulki ga malam Ibrahim Shekarau kuma shekarau ya shure su bayan ya hau karagar mulki.