Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce ministocin da aka rantsar a yau an zaɓo su ne bisa cancanta domin su taimaka wajen tafiyar da lamurran ƙasar.
Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi jawabi bayan rantsar da sabbin ministoci a fadar sa da ke Abuja.
Cikin lafazi yace “Ƴan Najeriya na sa ran za ku yi aiki mai inganci kuma za ku sauke nauyin da aka ɗora muku.” – In ji Tinubu
Ya ƙara da cewa “Dole ne ku yi aikin da zai sanya ƴan Najeriya su sake amincewa da gwamnati.”
Ya bayyana cewa akwai babban nauyi a kan sabbin ministoci ganin irin manyan alƙawurran da gwamnatinsa ta ɗauka.
Shugaban ya kuma buƙaci sabbin ministocin da su yi aiki ba tare da nuna banbanci ba, inda ya ce: ”An ba ku wannan matsayi ne ba domin ɓangaren da kuka fito ku jihonhinku ba, sai dai domin ƙasa baki ɗaya.”
A watan Afrilu ne shugaban na Najeriya ya miƙa wa Majalisar Dattijan ƙasar sunayen mutum 45 domin tantantancewa a matsayin minsitoci.
Bayan haka nan shugaban na Najeriya ya bayyana ma’aikatun da kowane minista zai riƙe gabanin ranar ta yau da ake rantsarwar.
Sai dai ko a ranar Lahadi, shugaban ya fitar da wasu sauye-sauyen da ya yi na ma’aikatu ga wasu sabbin ministocin.