Hukumar kula da Zirga-zirga Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta musanta jita-jitar da ake yi na fara daukar sababbin ‘yan KAROTA
Hukumar ta bayyana haka ne a yau, bayan da ta fahimci jita-jita ta yi yawa na fara ɗaukar sababbin jami’an
Hukumar ta ce ya zuwa yanzu dai babu wani umarni na ɗaukar sababbin ‘yan KAROTA
A don haka Hukumar ke jan hankalin jama’a da su yi watse da duk wata jita-jita da take yawo don gudun afkawa hannun ɓata-gari.
Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir, yace Kwamitin da ya kafa yana ci gaba da aikin tantance ma’aikatan Hukumar ta KAROTA, da zarar ya kammala za a duba yiwuwar daukar sababbin jami’an
A don haka, ake sanar da jama’a su kuji yaɗa labaran da ba shi da tushe balle makama