Rashin zuwan shugabannin kananan hukumomi ofis kesa maaikata rashin zuwa aiki,shugaban kungiyar maaikatan kananan hukumomi ta kasa reshan jahar kano kwamaret Abdullahi Muhammad gwarzo ne bayyana Hakan a yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa dake helikwatar karamar hukumar birnin
Kwamaret gwarzo yace a yanxu kananan hukumomi sun zama kufai saboda rashin zuwa aiki da ba ayi Hakan ne yasa yayi kira ga shugabannin da maaikatan dasu Mai da hankali wajen cika alkawarin dasu dauka a yayin kama aiki.
Shugaban kungiyar ya Kuma lasafto kadan daga cikin irin nasarorin da ya samarwa kungiyar kamar Gina babbar shalkwata, da ciyadda maaikatan kananan hukumomi zuwa matakin jahar, da Karin shekaru ga maaikatan,Sai walwala da inganta rayuwar su, daga karshe ya yi Kira ga gwamnatin jahar kano data Bawa kungiyar maaikatan kananan hukumomin hadin Kai da goyon baya.