Cibiyar kasa da kasa mai nazarin halin tattalin arzikin duniya KPMG ta yi hasashen cewa cikin wannan shekara ta 2023 matsalar rashin aikin yi za ta karu a Najeriya da kaso 41 cikin dari.
Cibiyar ta yi bayanin cewa za a samu karuwar wannan mizani ne sakamakon karuwar mutanen da suke neman aikin yi a hukumomin gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu.
Rahoton wanda cibiyar ta fitar kuma ta rabawa manema labarai ya nuna cewa, yanzu haka matsalar rashin aikin yi shi ne babban kalubale ga gwamnatin Najeriya a dai dai lokacin da bukatuwar al`umma ke kara danne ci gaban tattalin arzikin kasar.
Rahoton ya ce, ci gaban da tattalin arzikin kasar ke yi a halin yanzu ba zai iya daukar nauyin mutane miliyan 4 zuwa 5 ba da suke neman aikin yi a kasar a duk shekara.
Kamar yadda rahoton ya nuna matsaloli kamar na karancin masu zuba jari da kuma durkushewar masana’antu ba za su taba barin Najeriya ta iya shawo kan karancin aikin yi ba a tsakanin ’yan kasar cikin wannan shekara ta 2023.
Rahoton ya ci gaba da cewa a bisa alkaluman hukumar kididdiga ta tarayyar Najeriya ya nuna cewa an fara samun matsalolin rashin aikin yi a kasar ne tun daga 2018 inda mizanin ya kai kashi 23.1 yayin da a shekara ta 2020 ya gusa zuwa kaso 33.3, sai a shekarar bara ya kai kaso 37.7 sannan kuma ana hasashen zai kai kaso 40.6 cikin wannan shekara.
Haka zalika rahoton na KPMG ya bayyana cewa a shekarar badi ta 2024 rashin aikin yi a Najeriya zai iya kaiwa kaso 43 yayin da kuma hauhawar kayan masarufi zai kai kashi 20 bayan ya sauka daga kashi 20.3 cikin wannan shekarar ta 2023.
Ko da yake cibiyar ta yi hasashen samun farfadowa zuwa kaso 3 cikin dari a 2023 a fannonin sadarwa da harkokin kasuwanci da kuma na man fetur, wannan kuwa baya rasa nasaba ne kan irin matakan magance matsalolin tsaro da gwamnatin tarayyar Najeriyar ke dauka .
Rahoton cibiyar KPMG ya ci gaba da cewa a shekarar bara ta 2022, bangaren tattalin arzikin da bai shafi man fetur ba ya taka rawa sosai kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya sabo da bunkasuwar hada-hadar kashe kudade a cikin gida da al`umma suka yi a bangaren sufuri da sadarwa da harkokin inshora inda aka samu cigaba da kaso 4.85 cikin dari.
Yayin da bangaren mai kuma ya samu koma baya da kaso 19.22, lamarin da aka danganta shi da ayyukan bata gari masu satar mai da lalata bututun mai da kuma rashin zuba jari daga bangaren ’yan kasuwa na gida dana waje