Jam’iyyar APC a jihar Adamawa ta ce duk da Kaye da ta sha a hanun jam’iyar PDP a zaben shugaban kasa har yanzu tana jin cewa zata lashe zaben gwamnan jihar.
APC, wadda ke da ‘yar takara mace daya tilo a jihar – ta ce domin samun nasarar PDP a zaben shugaban kasa ba abu ba ne da zai tsoratasu.
Jami’in yada labarai na jam’iyyar a jihar, Muhammad Abdullahi, ya ce zaben gwamna daban, na shugaban kasa ma daban.
Ya ce,’’ Ba mamaki ba ne zaben gwamna yazo mu ci zabe, domin alkaluman zabe a Najeriya yanzu sun canja, duka bin da mutum ke tsammani ba haka ba ne don masu zabe sun waye sun san abin da suke so.”
Muhammad Abdullahi, ya ce duk da jam‘iyyar PDP ita ke mulki a jihar, suna fatan samun nasara a zaben gwamnan da ke tafe.
Sanata Aishatu Dahiru Binani, ita ce ‘yar takarar gwamna a jam’iyyar ta APC a jihar ta Adamawa, da ake mata hasashen samun nasara a zaben gwamnan da ke tafe.
Bisa ga dukkan alamu zaben gwamnonin fafatawa ce mai zafi da ke gaban dukkan ‘yan takarar gwamna na jam’iyu a kowacce jiha dake kasar nan domin kuwa dukkan su suna ganin cewa lokacin da za su samar da gwamna daga jam’iyunsu ya zo.
Ga jam’iyyar APC dai, idan har ta ci zaben gwamna, a jihar Adamawa za ta kafa tarihin samar da mace ta farko a matsayin gwamna a Najeriya.