Burkina Faso ta soke yarjejeniyar hadin gwiwar soji tsakaninta da kasar Faransa
Mahukuntan Burkina Faso sun kawo karshen yarjejeniyar hadin gwiwar soji da Faransa wadda aka kulla tun 1961, matakin da ke zuwa mako guda tak bayan da sojojin da ke jagorantar kasar suka bukaci jakadan Faransa da sojojin da ke tallafawa sojojin kasar a yaki da ‘yan ta’adda da su fice daga Burkina Faso.
A wata budaddiyar wasika da ministan harkokin wajen Burkina Faso ya karanta tace daga yanzu gwamnatin sojin kasar ta warware yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla da juna a ranar 24 ga watan Afrilun 1961.
Ta cikin wasikar ministan ya ce an baiwa sauran sojojin kasar Faransa da suka rage a Burkina Faso wa’adin wata guda su tattara nasu ya nasu su fice daga kasar, don kuwa yanzu bata bukatar su a cikin kasar.
Sai dai y ace Burkina Faso na sha’awar ci gaba da alakar mutunta juna ya kyautata alaka da Faransa amma nesa-nesa ma’ana dai kowa na kasar sa.