Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu ya yi magana a karon farko game da halin da Gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu yake ciki.
Jaridar This Day ta ruwaito Sanata Abdullahi Adamu yana cewa Mai girma Rotimi Akeredolu yana kwance a asibiti, har ta kai ba zai iya tabuka komai a yanzu ba.
Shugaban APC mai-mulkin kasa ya yi wannan bayani ne a zaman da yayi da ‘yan Majalisar NWC da shugabannin jam’iyya na jihohi.
Jam’iyyar APC ta tabbatar da halin rashin lafiyar da Gwamna Rotimi Akeredolu yake fama da ita, yana jinya a asibitin kasar waje.