Sunan Ministotin da ya karade kafafen sada zumunta na Bogi ne –Dattuwa Ali Kumo
An shafe tsawon rana guda ana yayata jerin sunayen wadanda ake cewa, Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya na shirin zaba a matsayin Ministoci, a kafofin sada zumunta na yanar gizo duk da yake babu wata majiya a hukumance da ta tabbatar da haka.
Wannan dai ba shi ne karon farko da aka fitar da jerin sunayen da hotuna na “sababbin Ministocin” ba tun bayan rantsar da Bola Tinubu a matsayin Shugaban kasa.
Duk da ana sa ran Shugaba Tinubu zai mika sunayen Ministocinsa ga Majalisar Dattawa nan ba da dadewa ba; amma wadanda su ka bayyana zuwa yanzu sun zama tamkar na fatan alheri ne ko yada farfaganda da wasu ke yi don tallata sunayen wasu gwanayensu.
Abun da ya fito fili a sunayen da a ka yayata da ba sunan wanda ya fitar da sanarwar kamar yadda ake gani a bayanai masu tushe daga daraktan labarai na ofishin Sakataren Gwamnati Willie Bassey ko ma kakakin Shugaba Tinubu, Dele Alake.
A hirar shi da Muryar Amurka, dan kwamitin gudanarwa na APC Dattuwa Ali Kumo ya ce ba bukatar gaggawa daga wadanda su ka yada bayanan marar sa tushe amma jerin hakika na tafe.
Za a jira a ga wadanda za su zama Ministocin Gwamnatin Tinubu da a ka ce ‘yan siyasa za su ci gajiya kuma za a yi la’akari da gudunmawa daga jiha ko shawarar gwamnoni maimakon yadda tsohon shugaba Buhari ya nada Ministocin sa bisa ga wadanda ya sani ko ya gamsu ya yi aiki da su.